WASHINGTON, DC —
Wani bom ya tashi da yammacin yau a kasuwar waya, dake garin Azare, a arewa maso gabashin Najeriya, inda aka ce kimanin mutane goma sha biyar ne suka mutu, wasu da dama kuma suka samu raunuka.
Wakilin muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad, yace a lokacin ta abun ya faru har lokacin rubuta wannan labarin babu jami'an, tsaro ko kuma masu agajin gaggawa a wurin.
Wannan shine karo na biyu da ake kai harin bom a garin na Azare, a cikin wannan watan da muke ciki, ko da yake mutanen da ake zargi da tashin wannan bom din suma jama'ar garin sun aika dasu lahira, ta hanyar konasu da rataya masu taya, a wuya.