Kungiyar maharba ta Jihar Adamawa ta musanta labaran dake bazuwa cewa wai jami’an tsaro sun kama shugaban maharban da ya jagoranci kwato wasu garuruwan jihar daga hannun ‘yan Boko Haram. Sakataren kungiyar yace wannan labarin ba gaskiya ba ne.
A wani gefen, su kuma ‘yan kato da gora ko Civilian JTF a Jihar ta Adamawa, sun ce sun a samun nasara a kokarin yakar ‘yan bindiga, kuma sun fara shiga dazuzzukan dake jihar
Daga Abuja, jam’iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta ce ba ta hana kowa tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ba, duk da ikirarinta na cewa shugaba Goodluck Jonathan shi ne dan takararta tilo. Wannan ya biyo bayan karar da farfesa Akasoba Duke Abiola ta shigar gaban kotu. Rufai Ahmed Alkali shi ne mai ba shugaban shawara kan harkokin siyasa
Sai dai jam’iyyar APC ta bakin tsohon gwamna Danjuma Goje na Jihar Gombe, ta sunsuno yiwuwar kawar da PDP daga mulki..