Taron Kasashen Kungiyar ECOWAS Masu Arzikin Man Fetur A Nijar

ECOWAS

A wannan Juma’a ake kammala wannan taro da wata sanarwar karshen taro mai kunshe da shawarwarin da za a gabatarwa gwamnatocin kasashe mambobin CEDEAO.

Kasashen yammacin Afrika sun fara gudanar da taro a birnin Yamai domin tattauna hanyoyin inganta ayyukan hakar man fetur da sauran albarkatun karkashin kasa.

Taron dai an gudanar da shi ne don neman hanyoyi ta yadda za a tunkari kabula da dama da ake da su a wannan fanni musamman idan aka yi la’akari da wasu sauye sauyen da zamani ya zo da su.

Taron da ake kira ECOMOF a takaice wani lokaci ne da kwararrun a fannin albarkatun karkashin kasa ke tattauna matsalolin da ake fuskanta a wannan fanni kamar yadda jami’i a kamfanin dillancin man fetur wato SONIDEP Malan Kabirou Zakari Oumarou ya mana karin bayani.

Zaman na wannan karo dake matsayin na uku na gudana a wani lokacin da manyan kasashen duniya ke kokarin dakatar da amfani da man fetur da iskar gas saboda haka mahalartansa ke tattauna wannan babban kalubale.

Dr. Umar Faruk Ibrahim babban sakataren kungiyar kasashen Afrika masu arzikin man fetur APPO na daya daga cikin wadanda suka halarci taron.

Tsayin daka akan aiki da ilmantar da ma’aikatan cikin gida na wadannan kasashe na daga cikin shawarwarin da kwararru suka bayyana a matsayin mafita a maimakon ci gaba da dogara akan huldar ayyukan hakar ma’adanai da kasashen da suka ci gaba.

A wannan Juma’a ake kammala wannan taro da wata sanarwar karshen taro mai kunshe da shawarwarin da za a gabatarwa gwamnatocin kasashe mambobin CEDEAO.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Gudanar Da Taron ECOWAS Na Kasashen Masu Arzikin Man Fetur A Nijar