Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun ECOWAS Ta Umurci Gwamnati Ta Biya Wata Mata Diyyar Naira Miliyan 30


Kotun ECOWAS ta umurci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta biya diyyar Naira miliyan 30 ga Helen Joshua bisa laifin kashe danta, Solomon Andy, da wani sojan Najeriya ya yi ba bisa ka'ida ba a shekarar 2017.

Kotun ECOWAS da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin a yanke hukuncin da ta yi yau Talata.

Wani soja mai suna Abel Ocheme, wanda ke aiki a Makarantar Sakandare ta Kaduna ne ya kashe Solomon, mai shekaru 30, a shekarar 2017.

Ocheme ya kashe Solomon ne a lokacin da yake dibar yashi daga wani kwalbati da ke kusa da ofishin sojan.

A yayin karar da aka shigar gaban kotun ECOWAS, mai shigar da kara, Helen Joshua, ta samu wakilcin Gloria Mabeiam Ballason, yayin da Maimuna Shiruta ta wakilci gwamnatin Najeriya.

A cikin hukuncin , kotun ta yanke hukuncin cewa kisan da aka yi wa Sulemanu wanda sojan ya yi yayin da yake bakin aikinsa“ba bisa doka ba ne, kuma na rashin tausayi ne, kuma a wulakance”.

Kwamitin mutum uku na kotun da mai shari’a Gberi-be Ouattara ya jagoranta, ya ci gaba da cewa, Tarayyar Najeriya ta gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta ba tare da la’akari da sashi na 1 da 4 da 5 da 12 na kundin ‘yancin bil Adama da na jama’a na Afirka ba wanda ya umurci kasar kare mutuncin kowace rayuwa.

A cewar kotun, babban abin wulakanci ne da kuma take hakkin bil Adam ga sojojin Najeriya da suka kwace gawar Solomon tare da barin ta cikin wani yanayi na lalacewa tun ranar 9 ga watan Yuni, 2017, daga lokacin da kisan ya faru har zuwa lokacin hukunci.

Don haka kotun ta umurci gwamnatin Najeriya da ta biya mai karar Naira miliyan 25 a matsayin diyyar kashe danta Solomon da aka yi ba bisa ka’ida ba.

Sannan kuma ta umarci gwamnatin Najeriya da ta biya karin Naira miliyan 5 a matsayin kudin jana'izar.

Kotun ta kuma umarci da a gaggauta sakin gawar marigayin ga iyalansa.

Da take mayar da martani kan hukuncin, mai shigar da kara, Helen Joshua, da take magana ta bakin lauyanta, Ballason, ta godewa kotun da ta tabbatar da cewa an yi adalci a cikin lamarin.

XS
SM
MD
LG