Taron AU Ya Cimma Yarjejeniyar Cinikayya

Shugaba Buhari Da Mahamadou Issoufou a Taron Kolin Kungiyar Tarayyar Afirka

Shugabanin kasashe da na gwamnatocin nahiyar Afirka sun bayyana ranar 7 ga watan yulin 2020 a matsayin ranar fara aiki da yarjejeniyar cire shingayen dake tsakainin kasashe don baiwa jama’ar nahiyar damar gudanar da harkokin kasuwanci ba tare da wata tsangwama ba.

A karshen zaman da suka gudanar ranar Lahadi a jamhuriyar Nijar, an zayyana sunayen kasashen da suka bada cikakken hadin kai domin fara zartar da yarjejeniyar kasuwancin da kungiyar tarayyar Afirka ta bullo da ita, da nufin bunkasa tattalin arzikin nahiyar.

Ya zuwa yanzu kasashe 54 ne suka saka hannu akan takardun yarjejeniyar ta Zlecaf, amma 27 daga cikinsu ne suka tabbatar da cewa sun shirya domin fara wannan sabuwar tafiya.

Domin baiwa kasashen dake jan kafa isasshen lokacin nazarin wannan tsari, taron shuwagabanin kasashen Afrika ya tsayar da ranar 7 ga watan Yulin 2020 a matsayin ranar da za a fara zartar da wannan yarjejeniya.

Shigar Najeriya sahun wadanda suka yi na’am da wannan yarjejeniyar wani mataki ne da ake kallonsa da matukar mahimmanci a bisa la’akari da karfin tattalin arzikin da ta ke da shi a yammacin Afrika yayin da wasu ke ganin a maimakon ci gaba kasar za ta fuskanci asarar kudaden shiga, amma mukaddashin ministan harokokin wajen Najeriya Mustapha Sulaiman na cewa gwamnatin tarayya ta dauki dukkan matakan kariya kafin yanke wannan shawara.

Kafin cire shingaye a tsakanin kasashe domin ci gaban harkokin kasuwanci, masana sun bayyana cewa akwai bukatar kasashen Afirka su bude iyakokinsu domin baiwa al’umomi damar kai da kawo ba tare da tsangwama ba, dalili kenan jamhuriyar Nijer a karshen mako ta soke maganar visa a tsakaninta da duk ‘yan kasashen Afirka.

Kasar Ghana ce aka zaba domin karbar ofishin sakatariyar hukumar kula da wannan yarjejeniyar kasuwanci, yayin da kasar Eritrea dake matsayin kasa daya tilo da ba ta saka hannu akan takardun yarjejeniyar ba ta bukaci a bata lokacin tuntubar bangarorin cikin gidanta kafin ta yanke hukuuncin karshe.

A yau ranar Litinin ce ke zama a matsayin ranar karshen taron shuwagabanin kungiyar AU zasu yi taro da kungiyoyin kasashen yankunan Afirka irinsu CEDEAO da sauransu.

Domin Karin bayani saurari rahotan Sule Mumimu Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron AU Ya Cimma Yarjejeniyar Cinikayya - 3'03"