A Jamhuriyar Nijar, yau shugaba Mahamadou Issohou ya jagoranci bikin wani taron tattara kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa wadanda za a yi amfani da su wajen dorewar wani shirin da aka yi wa lakabin da Projet SWEDD, mai hangen bunkasa ayyukan mata da ilimin ‘yan mata.
Lura da yadda zaman kashe wando da mata ke yi, yana mayar da hannun agogo baya a dukkan yunkurin da duniya ta ke yi don fitar da su daga kangin rayuwa, hakan ya sa banki duniya daukar dawaniyar shirin da nufin magance wannan matsala ta hanyar wasu ayyukan na musamman.
Shirin zai shafi kasashe irinsu Benin, Burkin Faso, Cote D’ivoire, Mali da Mauritania da Nijar da Chad.
Dubban mata ne suka samu aikin yi a tsawon shekaru 4 na wannan shiri, yayin da yawan ‘yan matan da ke karatun zamani ya ninka a dalilin projet SWEDD.
Hakan ya taimaka wajen magance matsalar mace macen mata masu juna biyu, dalili kenan gwamnatocin wadanan kasashe suka ga dacewar ci gabansa a mataki na biyu.
A cewar shugabar wannan projet a yankin Sahel Pr Mariatou Kone Miliyon 100 na dollar Amurka ne, ake bukata domin ci gaban wadanan aiyuka a tsawon shekaru 5 masu zuwa.
Ga rahoton Wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma da cikakken rahoton.
Facebook Forum