Yau ne shugabannin kasashe da na gwamnatocin Afirka suka fara gudanar da taro a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar a karkashin inuwar kungiyar AU.
Taron ya kunshi tattaunawa akan wasu muhimman batutuwa, cikinsu har da yarjejeniyar kasuwanci ta ZLECAF wacce ke cire shingayen da ke dabaibaye sha’anin tattalin arzikin wannan nahiya.
Da taken kungiyar tarayyar Afirka ne aka soma bikin bude taron.
Ita dai wannan kungiya mai shekaru 56 da kafuwa kasancewarsa wani lokaci na soma zartarda yarjejeniyar kasuwanci ta bai daya ZLECAF, wacce a karkashinta kasashen Afrika suka amince su cire dukkan wani takunkumin da ke kawo cikas wajen gudanar da harakokin kasuwanci a tsakaninsu.
Shugaban rikon kungiyar ta AU wato shugaban kasar Egypt Abel Fata Alsisi, da ke jawabin bude taron, ya yi fatan ganin yarjejeniyar ta soma aiki a zahiri a karshen wannan haduwa.
Shugaba Issouhou Mahamadou na Jamhuriyyar Nijar, wanda shi ne mai masaukin baki ya bayyana cewa, fara aikin wannan yarjejeniyar wani mataki ne da ke ba da damar soma mayar da hankali wajen wasu mahimman ayyukan da kasashen nahiyar ke hangen kaddamarwa anan gaba, cikinsu har da shirin shimfida layin dogo irin na zamani da shirin bude jami’ar hadin gwiwar kasashen Afrika.
Sauran muhimman batutuwa sun hada da batun bullo da dubarun sarrafa ma’adinan karkashin kasa, da shirin kafa kamfanin zirga zirgar jiragen sama na hadin gwiwa, da batun samar da fasfo (PASSPORT) daya tilo domin al’umomin wannan nahiya.
Ana sa jawabin kuma, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat ya bayyana cewa, samun nasarar yarjejeniyar ZLECAF wani abu ne da ba zai tabbata ba, muddin ba a sakarwa jama’a ‘yancin kai da kawo a tsakanin kasashen nafiyar ta Afrika ba, saboda haka ya yi kira ga shugabannin akan bukatar duba wannan batu.
A wunin farkon wannan haduwa kasashen Najeriya da Gabon da Equatorial Guinea da Jamhuriyar Benin sun rattaba hannu akan wannan yarjejeniyar abin da ke nufin a yau kasashe 27 ne suka amince a soma wannan tafiya.
Shugabannin kasashe da na gwamnatoci kimanin 30 din da suka halarci bikin bude wannan taro na ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu. Ana sa ran za su kira taron manema labarai a yammacin yau Lahadi.
Ga rahoton Wakilin muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum