Shugabannin kasashen Afrika 50 ne ake sa ran isar su a birnin Yamai ya zuwa jiya Juma’a, wuni daya bayan halartan ministocin harkokin wajen su, domin fara taron kolin a gobe Lahadi da za a tattauna batun cinikayya tsakanin kasashe ba tare da sanu tsaiko ba.
Idan Afrika ta hada tattalin arzikin kasashenta, ta kawar da shingayen cinikkayya da haraji, a cikin yarjejeniyar kara samar da ayyukan yi da kyautata rayuwa tsakanin al’ummar Afrika da yawanta ya kai biliyan daya da miliyan dari biyu, hakan zai sa Afrika tayi gogayya da sauran yankuna da ma duniya baki daya.
Yarjejeniyar cinikayyar ta samu bunkasa ne a farkon wannan mako, yayin da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nuna amincewarsa ga sanya hannu a kan yarjejeniyar a karshen wannan mako.
Shugaban kasar dake Afrika ta Yamma mai yawan al’umma da ta kai akalla miliyan 190 kuma mai karfin tattalin arziki, ya fada a wani sakon twitter cewa "ba shirin cinikayya kadai Afrika ke bukata ba, har ma da ajendar yin kaya a cikin nahiya".
Facebook Forum