AU ta bayyana cewar Shugabanta, Moussa Faki Mahamat, “ya bukaci shugabanni a yankin na yammacin Afrika su kara kaimi wajen tattaunawa tsakanin shugabancin kungiyar ECOWAS da kasashen uku”, wadanda a Lahadin data gabata suka zargi ECOWAS din da yin barazana ga matsayinsu na ‘yantattun kasashe.
A ranar Lahadin da ta gabata, shugabannin kasashen dake yankin sahel suka fitar da sanarwar da ke cewa batun ‘yanci ne yasa suka gaggauta ficewa da kungiyar ta ECOWAS ba tare da wani bata lokaci ba.
Dukkanin kasashen uku- wadanda aka kirkiri ecowas dasu a shekarar 1975 –an dakatar dasu daga cikin kungiyar inda Nijar da Mali ke fama da dimbin takunkumai a yayin da ECOWAS ke kokarin ganin sun maida mulki hannun farar hula cikin kankanin lokaci ta hanyar gudanar da zabubbuka.
“Akwai rashin tunani a cikin takunkumin kuma al’amari ne da baza’a amince da shi ba “a wannan lokaci da kasashen suka rungumi kaddararsu a hannuwansu”-a matsayin tsokaci ga jagororin juyin mulkin da suka hambarar da gwamnatocin farar hula.
A ‘yan watannin baya-bayan nan kasashen uku sun karfafa matsayarsu tare da hade karfinsu wuri guda karkashin” kawancen kasashen yankin sahel”.