Wani dan gwagwarmaya a kungiyar wayar da kan matasa gameda fa'idar Demokuradiyya, komorade Awwal Mohammed, yayi magana kan irin nasarori da yake ganin kungiyar hada kan kasashen Afirka ta samu.
A hira da yayi da Ibrahim Ka'almasi Garba, Mallam Awwal yace AU ta taimaka wajen sasanta tsakanin sojoji da suka yi juyin mulki da farar hula, inda aka kai ga mika mulki ga fararen hula cikin dan karamin lokaci.
Duk da haka komorade Awwal yace akwai bukatar kungiyar ta hoppasa wajen magance irin wariya ko kyamar baki da ta taso a Afirka ta kudu.
Komorade Awwal yayi kira ga kungiyar ta kara matsa kaimi kan shugabannin da suke mulki sai rai yayi halinsa, kamar yadda shuga Nkurunziza, na Burundi yake shirin yi.
Haka nan dan gwagwagrmayar yayi magana kan bukatar kare mutuncin 'yan Afirka.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5