Har yanzu dai babu tabbacin wake iko da kasar yayin da zanga-zangar siyasa da ake yi kullum a Bujunbura ke haddasa fada tsakanin bangarorin jam’iyyun adawa.
Wadanda suka shaida laamrin sun ce an gwabza mummunan fada yau Alhamis a kewayen ginin gidan redyo da na talibijin din kasar, wanda har yanzu ya ke hannun masu goyon bayan shugaban.
Kuma sashen tsakiyar Afrika na nan Muryar Amurka ya ba da rahoton cewa an rufe gidan rediyon Burundi wanda ke mallakar gwamnati.
Tunda farko, gidan rediyon ya gabatar da sakon shugaba Pierre Nkurunziza, wanda ya ce har yanzu shi ne yake kan mulki kasar kuma sojojin kasar suna goyon bayansa.
Babu tabbacin inda shugabaNkurunziza yake yayin da kamfanin dillancin labaran Faransa ya fadi cewa shugaban na wani wuri da ba’a fadi ba a birnin Dar es Salam na kasar Tanzaniya, inda ya halarci wani taron kasashen yankin game da al’amarin siyasar kasar jiya Laraba.