Janar Godefroid Niyombare, ya gayawa kafofin yada labarai masu zaman kansu cewa zai kafa wani kwamiti da zai maido da zaman lafiya da hadin kai a kasar. Wakilin Muryar Amurka, Gabe Joselow, wanda ke Bujumbura babban birnin kasar, yace mutane suna ta nuna farin cikinsu bayan wannan sanarwar.
Sai dai ya ce babu tabbacin ko Janar din na da cikakken goyon bayan sauran sojin kasar. Wakilin na Muryar Amurka ya kuma ruwaito ce sojojin sun yiwa gidan radiyon kasar kawanya, sannan an ji harbin bindiga a birnin, yayin da ‘yan sanda suke artabu da masu zanga zanga.
Masu adawa da burin na shugaban sun ce hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, yayin da masu mara mai baya suke fadin akasin hakan, saboda a cewarsu, ‘yan majalisu ne suka zabe shi a daya daga cikin wa’adin da ya yi, ba masu kada kuri’a ba.