An samu baraka tsakanin sababbin ‘yan majalisar wakilai dake da rinjaye cikin adadin ‘yan majalisar 360. Wasunsu na cewa ya dace su mara baya ga tsofaffin ‘yan majalisa su fidda sabon kakaki, inda wasu da dama ke cewa a’a, sabon dan majalisa ya dace a zaba, da zai tafi dai-dai da sabuwar gwamnatin Janar Buhari.
Sabon dan majalisa Ustaz Yunus, na gani sabbabin su jira har sai sun samu gogewa.
“Dole ne mu bi, tunda kaga mu sababbin ‘yan majalisa wanda ya shigo na tarayya a yanzu, akwai abunda ake cewa “ranking”, to dole ne sai kuma ka zama kana da kwarewa (experience). Ko mu da muka taho daga matakin Jiha, za’a ce to ai ilimin mu ba na matakin tarayya bane.”
Na kan gaba a sababbin ‘yan majalisar Muhammad Kazaure dake adawa da wannan manufa, yace ko shi kansa, zai iya jagorantar majalisar.
Yace “abunda ake nema shine ya za’a yi adalci? In gaskiya tazo a fito da ita? In karya tazo a bayyana ta? To kuma wadannan abubuwan ne aka rasa. Saboda haka kwararrun suna wajen, amma abubuwa da yawa an kawo an danne. Anzo maganar kudade, biliyan 20 ta bace, bamu ji ta ba.”
Wannan shine karo na farko da jam’iyyar PDP ta rasa rinjaye a majalisun biyu na tarayya, inda APC ta amshe rinjaye.
Your browser doesn’t support HTML5