Tun da sanyin safiyar Litinin dinnan ne ‘yan majalisar dokokin Jihar ta Ondo su 24 daga cikin 26 na jam’iyyar PDP suka bada sanarwar tsige mataimakin gwamnan Jihar Alhaji Aliyu Olasunusi daga kan mukaminsa.
A yau da safe ne dai wani kwamiti mai mutum 7 da babban alkalin alkalan jihar ya kafa su gudanar da bincike akan mataimakin gwamnan, bisa laifukan da ake zargin ya aikata, suka gabatar da rahoton su a gaban majalisar, inda suka ce sun samu mataimakin gwamnan da aikata wasu laifuka guda 7, kuma nan take majalisar dokokin Jihar ta amince. Shugaban majalisar dokokin Jihar Mrs. Jimoke Akindele ta zartar da kudurin tsige mataimakin gwamnan.
Sai dai kuma wakilan jam’iyyar APC guda biyu dake majalisar sun ki hallartar zaman majalisar na yau. Ita ma jam’iyyar APC ta bakin kakakin ta na kasa, Alhaji Lai Muhammed ta bayyana hanzarin tsige mataimakin gwamnan da aka yi, da cewa hakan ya sabawa tsarin demokradiyya.
Jam’iyyar APC ta kara da cewa, idan ana tsige mataimakin gwamna bisa laifukan sauya jam’iyya, shima gwamnan ya kamata a tsige shi, domin tare da mataimakinsa ya sauya sheka.
Mallam Abdu Abuja, wani mazaunin Jihar Ondo ne “wannan al-amari ne na son kai, saboda shi kanshi gwamnan ma, ai a wata jam’iyya yake.”
Masu lura da harkokin siyasar kudu maso yammacin Najeriya na ganin da kyar jam’iyyar adawa zata jure adawa a karkashin jam’iyyar APC dake shirin karbar ragamar mulkin Najeriya.