Hukumar ta shirya bitar ne wa akawunan majalisun dokoki da daraktocinsu.
Malam Ali Majiya daya daga cikin wadanda suka kula da taron ya bayyana makasudin shirya taron bitar. Yace su akawunan da daraktocinsu sun yi shekaru 15 suna aikin saboda haka sun san madafa da makaman aikin. Aikin majalisa ba'a koyas dashi a wata makaranta ko jami'a. A bakin aikin ake koyo har a iya.
Bitar ta shiyar Kano ta kunshi jihohi tara, wato Adamawa, Yobe, Gombe, Bauchi, Taraba, Katsina, Sokoto, Kano, da Jigawa.
Masana sun tabo alamura daban daban a wurin bitar da suka shafi ayyukan 'yan majalisu..Onarebu Lawal Burji na cikin wadanda suka gabatarda makala. Yace akwai wadda tayi magana akan tantance karfin iko namatakai guda uku na gwamnati, wato bangaren majalisa da bangaren zartaswa da kuma bangaren sharia da kuma yadda dan majalisa zai sani menene ma aikinsa a majalisa.Akwai kuma yadda zai aiwatarda aikin da yin muamala da wadanda suka zabeshi.
Bitar ta koyawa wadanda zasu je su koyawa 'yan majalisa ne. Abun da mahalartar bitar suka koya zasu je su tara sabbin 'yan majalisun da aka zaba su koya masu.
Akawun majalisar dokokin jihar Adamawa yace bitar tana koya masu yadda zasu fuskanci kalubalen da suke samu daga sabbin 'yan majalisun dokoki. Yace akwai wasu 'yan majalisun da basu yi karatu sosai ba kuma komi aka fada masu basa ganewa. Amma idan aka koya masa ya gane aikinsa zai zama a saukake.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.