Guguwar iskar rigimar siyasar shugabancin majalisar dokokin jihar Adamawa ta dauki sabon salo.
Majalisar ta sallami takwarorinta uku bisa ga laifin sauya sheka zuwa wasu jam'iyyu. Haka ma zaman doya da manja tsakanin majalisar dokokin jihar da kuma bangaren zartaswa ya kara kazancewa inda ya rikide zuwa na tonon silili wa bangaren gwamnati.
Majalisar tayi barazanar mika wasu takardu dake kunshe da bayanai na wani yunkuri na yin sama da fadi da wasu makudan kudade na kwagiloli wa hukumar yaki da zarmiya da cin hanci wato EFCC.
Gwamnati ta nemi ta sayi motoci biyu kacal a kan kudi nera miliyan dari da casa'in. An nemi a sayi wasu takardu da ake sayar dasu dubu daya da dari biyu a kasuwa akan dubu tara da dari biyar. Akwai wasu ire--irensu. Wanda ya hana a aiwatar da kwangilolin an ce an koreshi. Majalisar ta bada umurni gwamnatin ta mayarda mutumin bakin aikinsa domin samun irinsa nada wuya.
Kakakin majalisar Ahmadu Fintiri yace an bankado badakalar da bangaren zartaswar ya shirya na bada wasu kwangiloli na sama da nera miliyan dari biyar da hamsin.
Wannan abun fallasar ya fito fili ne lokacin da gwamnati ta nemi yin rufa-rufa ta hanyar sallamar Alhaji Bello Umar daraktan hukumar dake sa ido akan ayyukan kwagiloli bisa kin yadda ya sa hannu kan takardun kwagilolin.
Hudu daga cikin 17 na bangaren Onarebul Jerry Kundusi kakakin da bangaren gwamnati ya nada sun ce bada yawunsu aka aikata tsige Ahmadu Fintiri ba. Sun ce zasu bincika su gano yadda aka yi satar sa hannunsu.
Yayin da bangaren Ahmadu Fintiri ke zama a zauren majalisar, bangaren Jerry Kundusi kuma yana taro a gidan gwamnati.
Barrister Husseini Turaki Kazir yayi fashin baki akan bangarorin biyu na majalisar. Yace yadda aka tsige Fintiri doka aka taka. Yace har gobe Ahmadu Fintiri shi ne halartacen kakakin majalisar.
Ga rahoton Sanusi Adamu.