Da yake yiwa ‘yan kasar Nijar jawabin barka da zagayowar ranar samun ‘yancin kai ta ranar uku ga watan Agusta ne shugaban kasa Mahamadou Issouhou ya bayyana rashin gamsuwa da tafiyar sha’anin ilimi a kasar, wanda a cewarsa mizanin tabarbarewar wannan fanni ne ya haddasasa mummunar faduwar dalibai a jarabawar BREVET da BAC din da aka gudanar a watan yuni da yulin jiya.
Shugaban dai ya dora alhakin faruwar matsalar a wuyan dalibai da malamai saboda yawan shiga yajin aiki da yajin daukan karatu da suke yawan yi.
Sai dai a cewar Lawali Abubakar na kungiyar FPN shugaban ya yi tuya ya manta da albasa domin a ra’ayinsa gwamnati ce ke da alhakin dukkan abubuwan dake faruwa a fannin ilimi.
Aci gaban jawabinsa shugaban kasa ya kara tunatar da jama’a mahimmancin ilimi saboda haka ya gargadi masu hannu a sha’anin karatu musamman dalibai su dakatar da dukkan wata tarzoma don mayar da hankali akan karatu ta yadda nan gaba zai amfanesu da kuma al’uma.
To amma Abdou Idi na ganin yunkurin farfado da sha’anin ilimi ba zai yi tasiri ba muddin gwamnati tana biris da shawarwarin wadanda abin ya shafa.
Rashin biyan albashin malamai akan lokaci da jinkirin biyan kudaden alawus din dalibai da karancin malamai da na ajijuwan karatu ko kujeru da teburan zama a makarantu mallakar gwamnati na daga cikin tarin matsalolin da ke kokarin samun gindin zama a ‘yan shekarun nan a Jamhuriyar Nijar.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Your browser doesn’t support HTML5