Ta’addancin Paris Hari Ne Akan Wayayyiyar Duniya- Obama

Shugaban Amurka, Barack Obama yana halartar taron manyan kasashen duniya 20 a Turkiyya

Shugaban Amurka Barack Obama, wanda ke halartar taron manyan kasashe 20 ko kuma G-20 a Turkiyya, ya bayyana hare-haren ta'addancin da aka kai birnin Paris da hari kan wayayyiyar duniya

.Da babban taron na Shugabannin manyan kasashen zai raja'a ne kan cinakayya da makamashi da cajin yanayi; to amma ayanzu harin ta'addancin da aka kai birnin Paris ya rinjayi sauran dukkannin batutuwan.

Shugabannin sun fadi a daftarin sanarwar bayan taro cewa, "Da kakkausan harshe, mu ke yin tir da mummunan harin ta'addancin nan da aka kai birnin Paris abin ki ne ga dukkannin jinsin bil'adama.

Shugabannin kuma sun jaddada hadin kansu wajen yaki da ta'addanci na kowani irin nau'i a kuma duk inda ya faru.

Obama zai gana da Firaministan Burtaniya David Cameron, da Shugabar Jamus Angela Merkel da Firaministan Italiya Matteo Renzi da Ministan Harkokin Wajen Faransa Laurent Fabius a yau dinnan Litini.

Hakan nan a fruwa ne a daidai lokacin da baban taron da ake yi a garin shakatawar nan na Antalya ke kowa karshe.

Da Shugaban Faransa Francois Hollande ma zai halarci taron amma sai ya dakata a Faransar saboda harin ta'addancin da aka kai birnin Paris.