Sakataren harkokin wajen Ingila Philip Hammond yace kara daukan matakan tsaro masu tsanani sun kawo tafiyar hawainiya akan yadda ake fitar da 'yan kasarsa daga garin Sham el-Shaikh.
Dubban 'yan kasashen waje suke neman hanyar ficewa daga garin biyo bayan tarwatsewar jirgin Rasha ranar 31 ga watan jiya.
Duk da cikas din da aka samu Mr Hammond ya ce kimanin 'yan Birtaniya dubu bakwai ne suka fitar dasu kuma kafin karshen wannan makon zasu gama kwashe sauran.
Mayakan sa kai da suke da alaka da kungiyar ISIS sun yi ikirarin su ne suka kakkabo jirgin fasinjoji na kasar Rasha. Jirgin na dauke da fasinjoji 224.
A karon farko kuma Firayim Ministan Rasha Dimitry Medvedev yace tana yiwuwa 'yan ta'ada ne suka kakkabo jirgin. Furucin nasa shi ne na farko da wani babban jami'in Rasha ya amince 'yan ta'ada ne suka yi sanadiyar tarwatsewar jirgin.
Amma mahukuntan Masar dake binciken musabbabin hadarin sun ce basu cimma matsaya daya ba tukun akan abun da ya tarwatsar da jirgin.