Da yake magana a wani taron koli da shugabannin kasashe fiyeda 60 suka halarta daga Afirka da Tarayyar Turai, shugaba Holande yace, idan ba Tarayyar Turai ta tallafawa kasashen ba, matsalar kwarar bakin haure inda dubun dubatan mutane suke gudu zuwa Turai zai ci gaba.
Shugaba Hollande ya lura cewa galibin bakin hauren sun fito ne daga kasashen Sudan da Eritrea. Gameda Eritrea, yace tilas a "tsanantawa shugabannin kasar su sake hali. Yace "babu wanda yake magana kan batun kasar da take ci gaba da rasa al'umarta a karkashin idon baragurbin shugabanni, wadanda ba ruwansu."
Taron kolin da kungiyar hada kan kasashen Turai ta shirya na kwanaki biyu, Laraba da Alhamis a birnin Valletta na kasar Malta, yana maida hankali ne kan dalilan da suke sa mutane barin kasashensu na asali, da inganta hanyoyin kaura bisa doka, kara inganta hanyoyin kare bakin haure,yaki da 'yan fasa kwaurin bakin hauren, da kuma gyara hanyoyin hada kai da kasashen Afirka domin maido da mutanen da basu cancanci a basu mafaka ba.
Firayim Ministan kasar Belgium Charles Michel yayi kira da a dauki kwararan matakai. Ba ataron shan shayi a watse ba.