Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin Firayim Ministan Israila Zai Gana ada Shugaban Amurka


Shugaban Amurka Obama da Firayim Ministan Israila Netanyahu
Shugaban Amurka Obama da Firayim Ministan Israila Netanyahu

Firayim Ministan M Isra'ila Benjamin Netanyahu yana kan hanyarsa zuwa nan birnin Washington DC, a ziyararsa ta farko, tun bayan da Amurka da wasu kasashe biyar suka kulla yarjejeniya da Iran kan shirin Nukiyar kasar.

Yau Litinin ake sa ran Mr. Netanyahu zai gana da Shugaba Obama. Wannan taron shawarwari yana zuwa ne a wani lokaci "mai tsanani" ga Isra'ila wacce har yanzu kusan tana dimauce sakamakon yarjejeniyar Nukiliya da kasa da kasa ta kulla da babbar abokiyar gabanta Iran, da kuma tarzomar da kasar take fuskanta da Falasdinawa wadda babu alamar kakkauntawa.

Shugaban na Isra'ila ya nuna matukar adawa kan yarjejeniyar, har ya fusatar da Fadar White, lokacinda yayi jawabi a majalisar wakilanAmurka dake karkashin 'yan Republican inda yayi Allaha wadai da yarjejeniyar da a lokacin ake shirin kullawa.

Sa'o'i kamin ya tashi daga Isra'ila, Mr. Netanyahu yace ganawarsa da Mr. Obama zata fi maida hankali ne kan batutuwa da suka shafi yankin da kuma "karfafa tsaron Isra'ila.

XS
SM
MD
LG