Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya ta nemi A Yi Sauyi a Tsare Tsaren Kungiyar EU


Firai Ministan BIrtaniya David Cameron,Chatham House in London, Nov. 10, 2015.
Firai Ministan BIrtaniya David Cameron,Chatham House in London, Nov. 10, 2015.

A yau Talata, Firai ministan Burtaniya, David Cameron, ya yi kira ga kungiyar kasashen nahiyar turai, da ta samar da sauye-sauye, gabanin zaben jin ra’ayin mutane da kasar ta Burtaniya za ta yi na ko ta fice daga kungiyar.

Daga cikin bukatun da Cameron ya gabatar, akwai batun samar da kariya ga kasashen nahiyar da yawansu ya kai kashi daya cikin uku, wadanda ba sa amfani da kudin bai-daya na Euro.

Cameron ya kara da cewa, idan har, nahiyar za ta koma amfani da kudin na bai-daya baki dayanta, to Burtaniya ba ta cikin wannan tsari.

Ya kuma tabo batun cewa a samar da wani tsari da zai baiwa kasashen nahiyar damar kin amincewa da dokokin kungiyar da ba sa kare hakkokinsu.

Firai ministan na Burtaniya ya kara da cewa, yana goyon bayan tafiye-tafiyen ma’aikata a tsakanin kasashen, amma ya ce akwai bukatar gwamnatocin su samu karfin fada a ji, musamman kan batutuwan da suka shafi bakin haure.

2

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG