NIGER: Ta Yiwu Mazauna Kauyen Da Aka Kaiwa Sojojin Amurka Hari Na Da Hannu

Sabbin bayanai akan musayar wutar da aka yi a kudu maso yammacin Nijar har sojojin Amurka guda 4 suka rasa rayukansu na nuna cewa ta yiwu mazaunan kauyen sun taka rawa a harin.

Dakarun Amurka na musamman sun kammala wata ganawa kenan da shugabannin kauyen, suna takawa zuwa motocinsu, aka kai masu hari, a cewar wani jami’i, wanda ya yi magana da Muryar Amurka amma ya ce a sakaya sunansa tun da har yanzu ana kan gudanar da bincike.

Sojoji sun ce an kai lokaci mai tsawo ana ganawar, wasu ma na kyautata zaton cewa da-gangan ‘yan garin suka ki barin sojojin su bar garin da wuri, a cewar wani jami’i yau Laraba.

Harin da aka kai ranar 4 ga watan nan na Octoba akan dakarun Amurka da na Nijar ya faru ne a kusa da kauyen Tongo-Tongo dake yankin Tillaberi, a cewar ma’aikatar tsaron Nijar.

Nijar ta ce an kashe jami’an tsaron ta guda hudu a harin, tare da raunata wasu. Wasu sojojin Amurka 2 sun sami raunuka kuma an dauke su da jirgin sama zuwa Jamus don ayi masu jinya.