Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KENYA: An Hallaka Wasu Malaman Jami'ar Fasaha


Yau Talata aka kwashe wasu malaman jami’ar Fasaha ta kasar Kenya a lokacinda aka yiwa motocin su kwantan bauna a lokacinda suke tafiya a gabar tekun Indiya.

Shugaban 'yan sandan yankin Larry Kieng, yace ana jigilar wasu dalibai da malaman kwalejin fasaha ta Mombasa, daga gidajensu zuwa makarantar lokacinda wasu 'yan bindiga suka fito daga dajin dake kusa, suka bude musu wuta.

An jiwa direban motar da 'yan sanda guda biyu da suke raka daliban rauni a harin. Ba’a san ko su wanene 'yan bindigar ba, amma Larry Kieng, ya ce ana tsammanin 'yan yakin sa kan kungiyar Al-Shabab ta kasar Somaliya, suna da hannu a harin.

A halinda ake ciki kuma a fagen siyasar kasar shugaban ‘yan hamayya Ra’ila Odinga, ya janye daga zaben shugaban kasar da za’a sake yi cikin watan nan.

A wani taro da manema labarai yau Talata, Mr Odinaga yace “bayan da muka yi nazarin matsayar mu dangane da zabe mai zuwa, kuma bisa la’akari da bukatun ‘yan kasar Kenya, da yankin da kuma duniya baki daya, mun hakikance cewa janyewa daga zaben da za’a yi ranar 26 ga watan nan shine abunda yafi da cewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG