Wannan labari ya farantawa ‘yan kasar rai ganin cewa biyan kudaden wuta na daya daga cikin abubuwan da ke da wahalar gaske bias la’akari da irin tattalin arzikin kasar.
A cewar Malam Sufuyanu, wannan shiri da gwamnati ta yi domin taimakawa talakawa abin farin ciki ne kwarai da gaske, domin daya daga cikin matsalolin da ke addabar talakawa da ya kamata gwamnati ta duba itace tsadar wutar lantarki.
Wannan mataki da gwamnatin Nijer ta dauka zai fara aiki ne daga farkon watan Janairun shekara mai zuwa, hakazalika sanarwar ta tayi Karin bayanin cewa wannan atakin zai ba masu karamin karamin karfi damar cin gajiyar wutar lantarki yayin da nauyin biyan kudin wutar zai koma hannun manyan kamfanoni.
‘Yan kasar da dama sun bayyana ra’ayoyinsu musamman ganin yadda lamarin ya dade yana ci masu tuwo a kwarya koda shike wasu sun ce ai sun gani a kasa.
Domin Karin bayani saurari rahoton Haruna Mammane Bako.
Facebook Forum