Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun 'Yan Adawan Kenya Ya Janye daga Zaben Shugaban Kasa da Za'a Sake Yi


 Raila Odinga, jagoran 'yan adawan Kenya
Raila Odinga, jagoran 'yan adawan Kenya

Shugaban 'yan adawan kasar Kenya Raila Odinga ya sanarda janyewa daga zaben shugaban kasa da za'a yi ranar 26 ga wannan watan saboda wasu bukatunsu da yace ba'a cika ba. Tun farko kotun kolin kasar ta soke sakamakon zaben farko da ya ba shugaban kasar Uhuru Kenyatta nasara

Jagoran ‘yan adawan kasar Kenya, Raila Odinga ya janye daga zaben shugaban kasar da za a yi a zagaye na biyu.

Odinga ya fada a wani taron manema labarai cewa, sun dauki wannan matsayar ce bayan wata tattaunawa da suka yi dangane da zaben, lura da irin bukatun ‘yan kasar ta Kenya da yankin da kuma duniya baki daya.

Ya kuma kara da cewa, sun yi imanin cewa zai fi kyau idan jam’iyarsu ta janye daga zaben shugaban kasar, wanda za a yi a ranar 26 ga wannan wata na Oktoba.

A ranar 8 ga watan Agusta, kotun kolin kasar ta soke sakamakon zaben, wanda shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya lashe, bayan da kotun ta gano cewa hukumar zaben kasar ta tafka kurakurai.

Shi dai Odinga ya sha yin barazanar cewa zai kauracewa zaben, idan har ba a sauya wasu jami’an hukumar zaben kasar ba, wadanda ya zarga da tafka magudin.

Ya kuma nemi da a sauya kayayyakin aikin wasu cibiyoyin zabe, inda a jiya Talata ya yi ikrarin cewa babu wata alama da ta nuna cewa hukumar zaben na shirin aiwatar da wadannan sauye-sauye.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG