Madugun adawa na kasar Kenya, Raila Odinga, ya janye daga zaben shugaban kasa da za a sake gudanarwa.
Mr. Odinga ya fadawa taron ‘yan jarida a yau talata cewa, “a bayan da muka yi muhawara kan matsayinmu game da zaben dake tahowa, da nazarin muradun al’ummar Kenya, da wannan yanki da ma duniya baki daya, mun yanke shawarar cewa zai fi kyau ga jam’iyyarmu ta janye dan takarar shugaban kasarta daga zaben da za a sake gudanarwa ranar 26 ga watan Oktoba na 2017.”
Kotun koli ta Kenya ta soke sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 8 ga watgan Agusta wanda shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya lashe, tana ,mai kafa hujja da wasu abubuwa na magudi daga bangaren hukumar zabe ta kasar.
Odinga ya sha nanata cewa zai janye daga zaben da za a sake gudanarwa idan har hukumar zabe ba ta maye gurabun jami’an dake da hannu a magudin da aka yi lokacin zaben ba.
Ya fada a yau talata cewa ba su ga wata alama daga hukumar zaben cewa tana da niyyar yin gyaran da suka nema ba.
Facebook Forum