Fiye da mako daya da kwace garuruwan, Michika da Bazza a jihar, Adamawa, yanzu haka ‘yan kungiyar Boko Haram, na ci gaba da watayawa, yayin da rahotani ke cewa akwai gawarwaki, yashe a cikin garin Michika.
A wani taron manema labarai da wasu shuwagabanin al’uma a yankin, suka kira sun bayan cewa ‘yan Boko Haram, ke rike da garin Michika da Baza, bawai sojoji ba.
Wani da dan jarida da ya tsallake rijiya, da baya yace abun kunya ne, ace a kasar yanzu bamu da kayan yaki, yakara da cewa a yanzu haka ‘yan ta’addan da ake fafatawa dasu, suna shiga gidajen mutane, suna kwasan kaya da kona gidaje.
Wasu majiyoyin tsaro na bayana cewa dakarun Sojojin Najeriya, sun fafata da ‘yan Boko Haram a garin Baza, inda aka kashe wasu kwamandodin kungiyar ta Boko Haram biyu, yayin dasu kuma ‘yan Boko Haram, aka ce sun jirkita Sojoji, haka nan kuma sun nada wasu sabin Amirori, a yankin, Gulak da Shuwa da yanzu ke hannun su.
Your browser doesn’t support HTML5