Sojojin Nijar Sun Fafata Da Mayakan Kungiyar Boko Haram

Sojojin Cadi da Nijar sun kashe 'yan Boko Haram, Maris 19, 2015

Rundunar Sojojin Nijar ta bayyana sakamakon fafatawar da Jami'an tsaron kasar suka yi da mayakan Boko Haram, a 'yan kwanakin nan a yankin Diffa.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a birnin Yamai, tace a ranar Alhamis 8 ga watan Satumba wata nakiya da aka haka ta tashi da wata mota a tsawon kilomita 13 daga gabashin ‘kauyen Bora dake a yankin Diffa.

Sojoji biyu ne suka rasa rayukansu kana kuma biyu suka jikkata. Haka kuma a ranar Litinin 12 ga watan Satumba da kimanin karfe Goma da rabi na safe, wani rukuni na jami’an tsaro dake sintiri sunyi kicibis da ‘yan kungiyar Boko Haram da suka yi musu kwantan bauna a tsawon kilomita 6 daga ‘kauyen Tumur dake a Diffa.

A wani martanin da jami’an tsaro tare da taimakon rundunar hadin gwiwa ta Nijar da Chadi suka mayar, ya bayar da damar fatattakar ‘yan Boko Haram. Jami’an tsaro biyar ne suka rasa rayukansu, wasu Shida kuma suka jikkata.

An kuma kashe kimanin ‘yan Boko Haram 30, tare da kwace makamai masu yawa. Har yanzu dai jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a yankin da wannan lamari ya faru.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Nijar Sun Fafata Da Mayakan Kungiyar Boko Haram - 1'26"