Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Wanzar da Zaman Lafiya Ta Adamawa Ta Ziyarci Amurka


Taron Kungiyar Wanzar da Zaman Lafiya Ta Adamawa A Amurka
Taron Kungiyar Wanzar da Zaman Lafiya Ta Adamawa A Amurka

Kungiyar Adamawa Peace Initiative mai hankoron wanzar da zaman lafiya a yankin Adamawa, tayi wani taro a daya daga cikin dakunan taro na Majalisar Dokokin Amurka, inda ta bayyana cewa kwalliya ta biya kudin sabulu a ayyukanta.

Jami’ar Amurka dake a Yola fadar jihar Adamawa, American University of Nigeria, itace ta kafa wannan kungiya a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu da nufin shawo kan tashe tashen hankali da aka yi fama da shi, da ake alakantawa da banbacin kabila da addini.

Ganin irin halin kunci da jama’a suka shiga sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram da yayi sanadin rasa matsugunan dubban al’ummar jihar da kewaye, sai kungiya ta shiga gudanar da ayyukan jinkai inda take tallafawa ‘yan gudun hijira na cikin gida da muhimman ababan rayuwa da suka hada da kayan masarufi da koyawa mata sana’oi da kuma ilimantar da kananan yara.

Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron, akwai shugabar jami’ar Dr. Margee Ensing da membobin kungiyar wanzar da zaman lafiyar Bishop Stephen Ransom da Imam Dauda Muhammad Bello da kuma Hajiya Turai Abubakar wadanda suka bayyana muhimmancin zaman lafiya, hadin kan al’umma da kuma kyakkyawar zamantakewa da juna. A cikin jawabinta shugabar jami’ar tace, za a iya shawo kan matsalolin rashin aikin yi, talauci da koma bayan ilimi idan jami’oi da kuma kungiyoyi masu zaman kansu zasu kwaikwayi abin da kungiya wanzar da zaman lafiya ta Adamawan ke yi.

Kungiyar ta nuna hotunan bayanan bidiyo na irin ayyukan da suke gunarwa inda mata da kananan yara suka bayyana yadda shirin ya amfanesu.

XS
SM
MD
LG