A jawabinsa sarkin Gombe Abubakar Shehu ya godewa Allah wanda ya bashi damar rungumar aikin taimakawa 'ya'yan talakawa da marayu domin su samu ilimin zamani da na addini.
Yace ya dauki matakin ne ganin akwai yara fiye da miliyan daya da basa makaranta walau saboda talaucin da iyayen ke fama dashi ko kuma su yaran marayu ne basu da masu kulawa dasu. Yace a duk fadin duniya Najeriya ce tafi yawan yaran da basa makaranta. Dalili ke nan da yake kokarin kawo tashi gudummawar domin rage adadin yaran da basa makaranta.
Wasu iyayen yaran da suka halarci bikin sun godewa sarkin da taimakonsa. Jauro Hamma daya daga cikin iyayen ya roki Allah ya sakawa sarkin da alheri. Shi ma mataimakin gwamnan jihar Gombe ya gargadi mutane su yi koyi da irin halin da sarkin ya nuna.
Daya daga cikin yaran da suka ci moriyar shirin sarkin tayi jawabi a madadin sauran yaran. Sun godewa sarkin tare da yin alkawari ba zasu ba sarkin kunya ba.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.