Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Kira Matasa Su Tashi Su Maidowa Najeriya Martabarta


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yau Talata Shugaban Najeriya Muhammad Buhari yayi magana a Daura garin haihuwarsa inda ya kira matasan Najeriya su maidowa kasar maryabarta da kimanta ta hanyar neman ilimi da kishin kasa da aiki da dabi'un da zasu kawo hadin kan kasar.

Shugaban ya yi wannan kiran ne yayinda masu bautawa kasa da suke aiki a karamar hukumarsa ta Daura wajen su dari suka kai masa gaisuwa gidansa. Shugaba Buhari ya sake jaddada anniyarsa na tabbatar da hadin kan kasar da cigabanta.

Ya gargadesu su kasance masu kiyayewa da natsuwa yayinda suke kokarin cimma burinsu a duniya. Su gujewa duk abun da ka iya jawo rashin jituwa da tashin hankali da ka iya wargaza kasar.

Shugaban ya lura musamman da masu bauta wa kasa da suka fito daga yankin Niger Delta da kudu maso gabashin kasar kana ya yabawa tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon wanda a lokacinsa aka kafa shirin a shekarar 1973. Yace kodayaushe na ga Janar Gowon na kan gode masa saboda shirin wanda ya taimaka wurin hada kawunan 'yan Najeriya.

Daga bisani sai shugaban ya koma kan 'yan Niger Delta din cewa su fada wa 'yanuwansu da suke neman kafa kasar Biafra su manta da ita, wato abu ne da ba zai sabu ba, wai bindiga a ruwa.

Yace a matsayinsa na tsohon janar ya taka daga Degema, wani gari dake kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru. Haka kuma yayi watanni talatin yana yakin Najeriya da Biafra, yakin da ya lakume mutane kimanin miliyan biyu.

Yace shugabanninsu sun turasu su yaki Biafra ba wai domin kudi ba ko man fetur amma sabili da Najeriya.

Saboda haka idan wasu shugabannin kasar sun gaza ba 'yan Najeriya suka gaza ba, inji Buhari.

Yace ku fadawa 'yanuwanku dole mu cigaba da tafiya tare mu gina kasarmu. Tana da girma kuma albarkatunta sun ishemu duka, inji shugaba Buhari.

Da yayi magana a madadin 'yan bautawa kasar jami'insu dake Daura Mr. Egbewumi Adebolu ya godewa shugaban da yadda ya karramasu da karbarsu. Yace yawancin masu bauta wa kasar sun yadda da shirin shugaban na rage rashin aikin yi.

Mr. Adebolu ya kara godewa shugaban da kyautar shanu da buhunhunan shinkafa da kudi da ya basu domin su ji dadin bikin salla.

XS
SM
MD
LG