Sojojin Nijar Na Bukatar Sauya Tunani Don Kada A Zubda Jini - Masana

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Bayan karewar wa'adin da kungiyar ECOWAS ta baiwa Sojojin da su ka yi Juyin Mulkin Nijar, yanzu hankali ya koma kan taron da shugaban kungiyar ECOWAS, Shugaba Tinubu ya kira a ranar Alhamis.

Masana harkokin tsaro na ganin wajibi ECOWAS ta taka sannu, saboda a cewar shi idan yaki ya barke tsakanin ECOWAS da Nijer to abubuwa za su dakwalkwale.

Duk da fatali da bukatar amfani da karfin sojan da Shugaba Tinubu ya nemi amincewar Majalissar Dattijai, wasu na ganin hankalin shugaban ya fi karkata kan dawo da Jamhuriyar Nijar kan turbar dimokaradiyya ta hanyar amfani da Sojoji.

Saurari cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Nijar Na Bukatar Sauya Tunani Don Kada Su Bari A Zubda Jini - Masana