Sojojin Najeriya Sun Kashe Kasurgumin Dan Bindiga Halilu Sububu

Rundunar sojojin Najeriya ta "Operation Hadin Kai" a bakin aiki (Facebook/Nigerian Army)

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe wani fitaccen dan fashin daji mai suna Kachalla Halilu Sububu, a wani gagarumin farmaki da ta kai wa yan bindiga a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Babban hafsan hafsoshin tsaron Nigeria (CDS) Janar Christopher Musa ya tabbatar da cewa sojoji sun kashe Sububu a wani gumurzu da dakarun

Sububu, wanda shi ne babban jigo a yan fashin yankin, ya mallaki wani babban wurin hako maadinai a kauyen Dan-Kamfani, a karamar hukumar Anka ta Jihar Zamfara kuma ya mallaki dubban shanu a dajin Sububu.

Ya shahara wajen horas da wasu yan bindiga masu hadari da suka hada da Bello Turji, kuma an ce ya mallaki nagartattun makamai da motocin aiki a dajin.

Halilu Sububu