Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Caccakar Batun Tarewar Karamin Minista Da Manyan Hafsoshin Tsaro A Sokoto Don Yaki Da 'Yan Bindiga


Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya
Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya

Mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar rashin tsaro na kallon sanarwar shiirin tarewar minista da hafsoshin tsaron a Sakkwato, don kawar da ayyukan 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma a zaman kalaman siyasa, domin sun sha jin irinsu kuma ba su yi tasiri ba.

Wannan na zuwa lokacin da wasu hotunan bidiyo da 'yan bindiga suka fitar ke ci gaba da daukar hankulan 'yan Najeriya.

Wadannan fayafayen bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na facebook su na kara nuna wa a fili irin yadda yanayin rashin tsaro yake a wasu sassan arewacin Najeriya.

A saboda haka wasu ke ganin cewa sanarwar da ma'aikatar tsaro ta fitar cewa ministan kasa a ma'aikatar Bello Mutawalle da manyan hafsoshin tsaro za su tare a Sakkwato su jagoranci kawar da ayyukan rashin tsaro tamkar cin tuwon bana da miyar bara ne.

Farfesa Mu'azu Shamaki dan asalin Sabon Birni ne a gabashin Sakkwato, yankin da rashin tsaro ya kai intaha, yana ganin cewa, wannan maganar siyasa ce kawai domin in an tashi kawar da wadannan mutanen ba sai an zo Sakkwato an zauna ba, akwai kayan aiki da jami'an da za su iya aikin kawar da su.

A haujin wasu kuma, wannan abin fata ne duk da yake an sha jin haka amma ba a samu moriya ba, a cewar Bashir Altine Guyawa dan asalin yankin Isa a gabashin Sakkwato.

A jihar Kebbi ma dake makwabtaka da Sakkwato, wasu mazauna yankunan da ke makwabtaka da jihohin Zamafara da Neja, su na nuna fargaba akan shigar bakin barayi a yankin kamar yadda wani mazaunin Dan Umaru Alhaji Sani ya sheda wa wakilin Sashen Hausa.

To sai dai Gwamnan jihar Kebbi Dokta Nasir Idris Kauran Gwandu ya ce ba abin damuwa yanzu a yankunan domin gwamanatin sa tana karfafa gwiwar jami'an tsaro tare da 'yan banga wadanda ke kama musu aiki.

Da yawa mazauna wadannan yankuna na kudancin Kebbi yanzu suna gudanar da lamurran su cikin zaman lafiya, in banda wannan korafin da wasu suka yi yanzu na shigar bakin barayi.

Wannan shirin da ma'aikatar tsaro ta Najeriya ta ayyana zata yi, idan har da gaske ne za a yi jama'a na ganin akwai bukatar ayi da gasken kar a fara a bari 'yan ta'adda su mayar da ramuwar gayya ga talakawa, kamar yadda ya sha faruwa a baya.

Ga sautin rahoton Muhammad Nasir daga Sakkwato:

Ana Caccakar Batun Tarewar Karamin Minista Da Manyan Hafsoshin Tsaro A Sokoto Don Yaki Da 'Yan Bindiga.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG