Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Ma’aikatan Jinya 2 A Wani Asibitin Kaduna


Yan bindiga
Yan bindiga

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya bayyana cewa rashin sadarwar waya a yankin Birnin Gwari ne ya hana mazauna yankin sanar da ‘yan sanda game da harin.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun sace wasu ma’aikatan jinya 2 yayin wani hari dasu kai kan wani karamin asibiti dake mazabar Kuyallo ta karamar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna.

Rahotanni na cewa ‘yan fashin dajin sun afkawa kauyen ne a jiya Litinin inda suka kaiwa karamin asibitin hari tare da yin awon gaba da wasu ma’aikatan duba gari guda 2.

Wani shugaban al’umma ya shaidawa tashar talabijin ta Channels cewar ‘yan bindigar sun yi niyar afkawa wata firamaren gwamnati ne tunda fari, amma da suka tarar babu ko dalibi guda a makarantar, sai suka hari asibitin tare da yin garkuwa da ma’aikatan 2.

Majiyar ta kara da cewa, ana fargabar ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu marasa lafiyar dake kwance a asibitin yayin harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya bayyana cewa rashin sadarwar waya a yankin Birnin Gwari ne ya hana mazauna yankin sanarda ‘yan sanda game da harin.

Sai dai, ya bayyana cewar wata jami’an ‘yan sanda na bin sawun ‘yan bindigar domin kamasu tare da kubutar da mutanen da suke garkuwa dasu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG