Rundunar sojojin Najeriya shiyya ta biyu karkashin hadaddiyar rundunar arewa maso gabas, wato Operation HADIN KAI ta samu nasarar cafke wani mutum mai suna Yusuf Sale wanda ake tuhumar shi da haramtacciyar sana'a ta samar wa da y'an Boko Haram takin zamani samfurin Urea a kauyen Bayamari, da ke karamar hukumar Geidam a jihar Yobe.
Rundunar ta cafke shi ne da buhu 38 masu nauyin kilo hamsin kamar yadda wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun Darektan hulda da jama’a Birgediya Onyema Nwachukwu.
In za'a iya tunawa a baya dai gwamnati ta haramta mu’amala da takin zamani samfurin Urea a yankin saboda 'yan ta'adda na amfani da shi wajen hada bama-bamai da ke illa ga jama'a gami da jamian tsaro. A halin yanzu dai jami'ai na zurfafa bincike akan shi wannan mutumin.
Tuni dai babbar shalkwatar hukumar sojin ta kasa ta yabawa dakarun saboda hazakarsu da kuma gaggawar cafke wadda ake tuhumar.
Bugu da kari, ta kuma bukace su da kada su shagala domin ganin karin nasarorin da suke samu kan y'an ta'adda ta hanyar mika kansu da iyalensu ga sojojin a kullum.
Rundunar sojin a karkashin jagorancin babban Hafsan Hafsoshin sojojin kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya na tabbatar wa dukkan masu bin doka da oda cewa rundunar tana kara himma domin kawo karshen ta'addancin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP har zuwa maboyarsu.
“Muna kuma kira ga mutanen arewa maso gabas da su taimaka mana da muhimman bayanai domin kawo karshen ta'addanci da tashin hankali a yakin da kuma kasa baki daya.”
In za a iya tunawa dai ko a baya said da sojojon suka cafke wasu mutane a kauyen kukareta dake gabashin Dramaturgy fadar jihar yoben dake Samarawa Mayakan Boko Haram da man fetur.
Kana a kauyen Katarko. Da Gujba ma an kame wasu dake samarwa Boko Haram Bayanai dangane da kai komon Dakarun, da kuma hakan sau tari ke Illa ga Dakarun