Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaro: Gwamna Zulum Ya Dakatar Da Ayukan Kungiyar Sa Kai Ta ACTED Ta Kasar Faransa


Gwamna Zulum (da jar riga) yayin da yake rangadin hanyar Mulai-Dalwa (Facebook/Borno state government)
Gwamna Zulum (da jar riga) yayin da yake rangadin hanyar Mulai-Dalwa (Facebook/Borno state government)

Gwamnan ya tabbabarwa kungiyar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba su goyon baya da hadin kai su ci gaba ayyukansu, idan har za su bi tsarin dokar kasa da kudurorin gwamnati kan sha'anin tsaro.

Gwamnan Jihar Barno da ke Arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagan Umara Zulum, ya ba da umarnin gaggawa na dakatar da ayyukan kungiyar sa kai ta kasar Faransa 'ACTED' a jihar.

Hakan ko ya biyo ne bayan da aka gano cewar Kungiyar ta kasa-da-kasa tana koyawa wadansu mutane yadda ake harba bindiga a wani Otel dake birnin na Maiduguri a ranar Asabar.

Mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau ne ya sanar da wannan matakin akan Kungiyar, bayan da aka kama masu bada horon da bindigogin roba da na’urar kwaikwayo a harabar wani hotel dake tsohuwar unguwar GRA a Maiduguri babban birnin jihar.

Jami’an rundunar ‘yan sandan da ke kula da yankin sun kai samame kan ‘yan kungiyar bayan da wasu jami’an gwamnati suka sanar da su cewar mazauna unguwar da ke makwabtaka da Otel din sun kai rahoton cewa suna jin karar bindiga daga harabar Otel din.

Gusau ya ce ‘yan sanda sun sami bindigogi biyu a Otel din sannan kuma yanzu haka suna tsare da mutum biyu masu ba da horon, dukansu ‘yan Najeriya, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Sanarwar ta bayyana cewa, a dalilin haka ne yasa Gwamna Babagana Zulum ya bada umarnin dakatar da ayyukan jinkai da kungiyar ta ACTED take bayar wa a Jihar ta Barno, sannan an rufe Otel din har sai zuwa lokacin da aka kamala gudanar da binciken.

Gwamnan ya tabbabarwa kungiyar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da basu goyon baya su ci gaba da gudanar ayukansu, idan har za su bi tsarin dokar kasa da kudurorin gwamnati a duk fadin jihar.

Wannan ba shine karo na farko da ake zargin kungiyar jinkai asalin karsar Faransa kan sabawa dokokin tsaro ba.

Ko a ranar 18 ga watan Satumba na shekara ta 2019, Rundunar Sojin Najeriya ta zargi kungiyar da da agaji ta ACTION AGAINST HUNGER da kuma dakatar da ayyukanta a jihohin Barno da Yobe, bayan da ta zarge su da baiwa 'yan kungiyar Boko Haram agaji da tallafin abinci da magunguna.

Zuwa yanzu, ‘yan sanda suna nan suna gudanar da binciken al’amarin

Ya

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG