Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Mayakan Boko Haram, ISWAP Suke Mika Wuya – Dakarun Najeriya


Wasu mayaan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)
Wasu mayaan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya)

Rundunar sojin Najeriya ta ce ana samun karin mayakan Boko Haram da na ISWAP da ke ajiye makamansu su mika wuya.

Hakan na faruwa ne yayin da dakarun kasar karkashin “Operation Hadin Kai” suke ci gaba da fadada ayyukansu a arewa maso gabashin kasar, inda suke kai hare-hare ta sama da kasa.

“Hare-haren bama-bamai da ake kai wa babu kakkautawa akan maboyar ‘yan ta’addan da ke dajin Sambisa da kewaye sun samar da sakamako mai kyau domin ‘yan ta’adda 56 da iyalansu sun ajiye makamansu sun mika wuya.” In ji Kakakin sojin Najeriya Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar, kungiyoyin ‘yan ta’addan sun fuskanci koma-baya an kuma kashe da yawa daga cikinsu “saboda hare-haren da jaruman dakarunmu suke kai wa.

Wasu daga cikin makaman da aka kama a hannun mayakan Boko Haram (Facebook/Dakarun Najeriya)
Wasu daga cikin makaman da aka kama a hannun mayakan Boko Haram (Facebook/Dakarun Najeriya)

"A ranar 4 ga watan Augusta, 2021, mayakan ‘yan ta’adda maza 18, sun mika wuya tare da makamansu da iyalansu ciki har da manyan mata 18 da yara 19 daga kauyen Chingori da kewaye da ke dajin Sambisa.”

Daga cikin makaman da aka karba a hannun ‘yan ta’addan, akwai, AK 47 guda biyar, da wata AK 47 kirar kasar waje, da na’urar hangen nesa, da gidan harshen AK 47 guda 8 da kuma kudi N7,700.

Makonni biyu da suka gabata, mayakan Boko Haram da na ISWAP sama da 100 sun mika wuya tare da iyalansu bayan jerin hare-haren da dakarun Najeriya suka yi ta kai masu, a cewar rundunar sojin Najeriya.

XS
SM
MD
LG