A wani sabon yunkuri domin kawo karshen ta'adancin a arewa maso gabas sojojin Najeriya sun kai samamen bazata kan sansanonin kungiyar Boko Haram
WASHINGTON, DC —
Da alama yanzu sojojin Najeriya sun yi damarar kawar da kungiyar Boko Haram daga kasar gaba daya musamman daga arewa maso gabas ganin irin samamen da suka kai kan sansanonin 'yan ta'adan.
Sojojin sun ratsa duk hanyoyi da kauyukan da 'yan ta'adan ke bi har suka bulla dajin sambisa inda kungiyar ta yi kakagida. Ganao sun sheida cewa sojojin sun fa kashe 'yan ta'adan da dama da su da mazansu da mata da yara. Sojojin sun kuma kona motocinsu da dama da kayan yaki. Al'ummomin dake kauyukan sun tabbatar cewa yanzu kam hankalinsu ya soma kwantawa.
'Yan ta'adan an ce sun fara gudu suna arcewa daga sansaninsu da wasu kauyuka da suka mallaka sabili da dimbin sojoji da suka fantsama dajin da kauyuka da wasu wuraren. Wani wanda ya shiga dajin sambisan amma ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da nasarorin da sojojin ke samu. Yace ya ga motoci da dama da aka kona banda gawarwakin maza da mata da yara dake warwatse a dajin. Mutumin ya kara da cewa a cikin daji 'yan Boko Haram suna da abinci da asibitoci da rijiyoyin burtsatsi da dama wadanda duk an konesu ko an lalatasu. Sojoji sun kuma cafke inda suke adana kayan yakinsu.
Haka ma ganao din yace akwa 'yan bindiga da yawa da aka raunata yayin da wasu suka gudu suna cewa sun gama jihadi. Wani da bai gama mutuwa ba yace maigidansu yace tunda aikin Allah ya kare kowa ya ajiye makamansa ya koma gidansa. Shi wannan ya tabbatar da cewa akwai wadanda suka samu suka fita da ransu daga dajin.
Amma a wasu sassan jihar Adamawa ana samun harin sari ka noke lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta kafa kwamitin tallafawa wadanda harin ke shafa. Malam Ahmed Sajo kakakin gwamnatin jihar ya bayyana matakan da ake dauka. Yace gwamnati tana son ta sani mutane nawa ne abun ya rutsa dasu kuma kimanin dukiyoyi nawa suka salwanta domin a san irin tallafin da za'a bayar.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5