Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari ga Garin Fota a Jihar Adamawan Najeriya Inda Suka Kashe Wani Dan Sanda


Yan sanda da sojoji sun bazama cikin daji domin neman wadanda suka kai hari ga garin Fota a jihar Adamawa.

Yan bindiga sun kai hari ga garin Fota a cikin jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya inda suka kashe wani dan sanda dan asalin garin na Fota wanda yazo hutu daga jihar Delta inda yake aiki.

Kakakin yan sandan Jihar Adamawa DSP Muhammad Ibrahim,yace rahoton da aka ce an kashe yan sanda bakwai, yace ba haka bane, dan sanda daya aka kashe da kuma jiwa daya rauni.

An kuma kashe ,mutane hudu da kona ofishin yan sanda, da kotu dakuma chohi guda biyu.

zaton,da akeyi wai ko sun kwashi makamai a ofishin yan sanda,kakakin yan sandan yace basu tafi da makami ko daya ba.

Yanzu kuma yan sanda da sojoji sun bazama cikin daji domin turo keyan wadanda suka aikata wanan mumunan aiki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG