A harin da suka kai a garin Fatan jihar Adamawa 'yan kungiyar sun yiwa garin diran mikiya inda suka fara da ofishin 'yansanda. Nan take suka kashe wasu 'yansanda bakwai, suka kone ofishinsu kafin su wuce wani Coci inda suka yi barna. Bayan haka sun kone kotu da coci guda uku.
A kan hanyarsu ta komawa 'yanbindigan sun ratsa wani kauye kusa da Fatan da ake kira Bisir inda ake gudanar da wani shagalin bikin aure. Sun hallaka mutum daya kana sun raunata wasu.
Wani jigon jam'iyyar PDP kuma tsohon malami a makarantar horas da sojoji Dr Umar Abdu yace akwai abun dubawa kan yawan hare-hare da 'yan Boko Haram ke kaiwa musamman a arewa maso gabas. Yace wannan lamarin nuni ne cewa gwamnati ce ta kasa. Shugaba ne bai iya ba. Yace yaya aka yi makamai na shigowa daga kasashen waje alhali kuwa gwamnati ce ke da hukumar kwastan. Yakamata a kira shugaban hukumar kwastan ya zo ya yi bayani. Hakama shugaban hukumar shige da fice ta kasar ya zo yayi bayani domin an ce yawancin 'yan Boko Haram ba 'yan Najeriya ba ne. A binciki duk shugabannin jami'an tsaro na kasar. Gwamnati ce ke da kudin da zata yi bincike ita ce kuma ke da ikon yin hakan.
Amma duk da abubuwan dake faruwa rundunar sojojin Najeiya tace tana samun galaba kan 'yan tsageran. To amma lokaci ne zai tabbatar da wannan ikirarin.