Kungiyar malaman Najeriya ko NUT a takaice ta nuna damuwarta domin yawan hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa kan daliban da basu san hawa ba bare sauka. A wurin manema labarai a garin Yola shugaban kungiyar na jihar Adamawa Dauda Maina ya kira gwamnatocin jihohi da na tarayya da su dauki matakan kare dalibai ta hanyar kare makarantu da katanga da jifge jami'an tsaro.
Dauda Maina yace a matsayinsu na malamai suna cike da bakin ciki domin haka duk makarantu a shingesu gaba daya a kafa kofar shiga da kofar fita a kowace makaranta kana a ajiye jami'an tsaro. Yace barin makarantu ba shinge ya sa banbance dan makaranta da bako ya yi wuya. Amma idan an shinge makarantu za'a san wanene ya shiga wanene ya fita. Yace a girke jam'an tsaro a kofofin da duk kusurwowin kowace makaranta. Yace suna cike da bakin ciki kuma suna rokon gwamnatin tarayya ta ceci mutanen arewa. Maganar tsaro ta wuce duk yadda mutum ke tsammani.
Kukan malaman na zuwa ne yayin da jami'an kwalagin horas da malamai ta jihar Adamawa ke kokarin rufe makarantar biyo bayan wasikun da aka ce an rubuto ana barazanar kai hari a makarantar. Ko ita ma rundunar soja a jihar ta bada shawarar a rufe kwalagin.
Dr Nelson Pongiri shugaban kwalagin yace sabili da wasu dalilan tsaro idan an yi misali da abun da ya faru a Buni Yadi da kuma wasiku biyar da suka rubuta masa dole su rufe makarantar. Yace bayan sun kai hari Gombi sai suka aiko masa da wasika cewa shi ne zasu kawo ma hari. Yace shugabansu Abubakar Shekau da kansa ya rubuta wasikar yana fada masa ya shirya suna zuwa. Ganin haka ya gana da malamansa suka yanke shawarar dalibai su tafi gida.
Ga karin bayani.