Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram ta Jefa Rayuwar Jama'ar Jihar Borno Cikin Mawuyacin Hali


'Yan gudun hijira a jihar Borno
'Yan gudun hijira a jihar Borno

Hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a jihar Borno ba dare ba rana sun jefa rayuwar jama'ar jihar cikin mawuyacin hali.

Yawan hare-hare da kungiyar Boko Haram ke kaiwa cikin jihar Boron sun raba jama da yawa da muallansu inda wasu ma suna kwana kan duwatsu domin tsira da ransu.

Irin hare-haren da 'yanbindigar ke kaiwa a kauyuka sun jefa mutane cikin wani halin kakanikayi da rashin sanin tabbas yaya zasu kare. Lamarin yayi sanadiyar kwararowar jama'a daga kauyuka zuwa cikin birane musamman birnin Maiduguri. Kowace safiyar Allah mata da yara kanana kan tako daga kauyukansu suna shiga garin Maiduguri koda ma basu da wani takamaiman masauki. Da yawa sukan kwana ne a kofar shagunan jama'a ko kuma cikin jidajen da ba'a gama ginasu ba. Wasu sukan samu mafaka a gidajen 'yanuwa da abokan arziki lamarin da ya sa ana iya ganin mutane takwas zuwa goma a daki daya.

Mutanen, dole ce ta sa suka fito domin kungiyar Boko Haram, bayan ta kashe maza magidanta da maza matasa sai kuma ta cinnawa gidajensu wuta wani zibin ma har dakone kauyan kocokan. Mata da yara kanana da suka saura da wadanda suka tsallake rijiya da baya su ne dole sai su gudo zuwa Maiduguri inda suke fatan samun tsaro. Wasu ma da harin bai kai kauyensu ba suna yiwa kansu kiyomanlaini domin maharan duk lokacin da suke so suke kai hari ba tare da samun wani cikas ba.

Kawo yanzu dai duk kauyukan dake kusurwowi hudu da suka shiga Maiduguri aka kaima hari. 'Yan kadan din da suka tsira duk sun fice. Umaru Likita daya daga cikin irin mutanen da suka fice daga kauyensu yace ganin hare-haren na kara faruwa kullum ya sa suka fice. Suna fargaban rashin tsaro dole suka bar gidajensu. Umaru Likita ma'aikacin makarantar sakandare ta gwamnati ne a Gwozah inda ya bar gidanshi da iyalansa da 'yanuwa. Kawo yanzu dai wurin wani abokinsa yake.

Ko a cikin Maiduguri akwai wasu a bakin hanya inda suke kwana saboda babu wurin mafaka. Wasu mata da yara marayu suna cikin gidan da aka kone. Sun ce basu da uwa ko uba domin dukansu an kashe su.

Kwararowar jama'a cikin Maiduguri ya yi sanadiyar karancin gidaje a birnin. Wani mai harka kan gidaje yace sun yi karanci da yawa mutane kuma na shan wahala kan neman inda zasu samu su tsuguna.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG