Sojojin Moroko Da Kungiyoyin Agaji Suna Aikin Ceto Mutane Daga Buraguzon Girgizar Kasa

Bayan wata mummunar girgizar kasa Morocco, sojoji da masu aikin agaji na tono mutane

Sojojin kasar Morocco da tawagar agaji a cikin manyan motoci da jirage masu saukar ungulu na ci gaba da kokarin ceton mutane daga karkashin buraguzo, bayan da wata mummunar girigizar kasa ta afka ta kuma kashe sama da mutane 2,400,

WASHINGTON, D. C. - Mummunar girgizar kasa da ta yi sanadin asarar rayukan dubban mutane ta jefa wadanda suka tsira da ransu cikin rudani suna neman agajin neman ‘yan uwansu da ake fargabar sun makale a karkashin baraguzan gine-gine.

Bayan girgizar kasa a Morocco

Ya zuwa yanzu dai jami'an kasar Morocco sun karbi tallafin da gwamnati ta bayar daga kasashe hudu ne kawai, Spain, Qatar, Birtaniya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, amma kuma wasu kungiyoyin agaji na wasu kasashen waje sun ce suna jiran izinin turawa ne.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Morocco ta ce jami'ai na son kauce wa rashin hadin kai wanda zai iya janyo koma baya a tsarin .

Morocco Satumba 10, 2023.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutane 300,000 ne girgizar kasar mai karfin maki 6.8 ta afku a daren ranar Juma'a, wadda zurfinta ya sa ta kara yin muni.

Morocco, Satumba 11, 2023.

Mafi yawan barna da mace-macen sun faru ne a lardin Al Haouz da ke tsaunukan Atlas, inda gidaje suka dunkule daya-bisa-daya da kansu, yayinda baraguzan gine-gine su ka toshe tituna. Wani lokaci mazaunan wurin ne ke aikin kawar da duwatsu da kansu.

-AP