Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa: Afghanistan Na Neman Kasashen Duniya Su Kai Mata Dauki


Wani jirgin na kai dauki a yankin Afghanistan
Wani jirgin na kai dauki a yankin Afghanistan

Ruwan sama da aka tafka da laka da ke kwarara suna haifar da cikas ga ayyukan ceto da ake gudanarwa, lamarin da har ila yau ya tilasta iyalai da dama suka kwana a waje.

Kungiyar Taliban a kasar Afganistan ta nemi agajin kasa da kasa yau alhamis, a daidai lokacin da kasar wacce yaki ya daidaita, ke kokarin tunkarar bala'in girgizar kasa da ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 1,000, da jikkata wasu da dama tare da lalata gidaje kusan 2,000.

Girgizar kasar mai karfin maki 6.1 ta afku ne a gabashi, da kudu maso gabashin kasar Afghanistan da kan iyakar Pakistan a safiyar jiya Laraba.

Jami’ai sun ce bala’in ya binne iyalai baki daya, da suka hada da mata da kananan yara, a karkashin baraguzan gine-ginen da ke lardunan Paktika da Khost da suka fi fama da bala’in.

Ruwan sama da aka tafka da laka da ke kwararar suna haifar da cikas ga ayyukan ceto da ake gudanarwa, lamarin da har ila yau ya tilasta iyalai da dama suka kwana a waje.

Babban jami’in kiwon lafiya a Lardin, Hematullah Esmat, ya fadawa kafafen yada labaran yankin cewa akalla iyalai 3,000 na bukatar agajin gaggawa a yankin na Patika.

XS
SM
MD
LG