Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Girgizar Kasa Ta Kashe Mutane Akalla 5,000 A Turkiyya Da Siriya


Girgizar kasa a Turkiyya
Girgizar kasa a Turkiyya

Da safiyar yau litinin wata Girgizar kasa mai karfin 7.8 a ma'auni ta kashe mutane sama da 2, 300 a kasashen Turkiyya da arewacin Siriya, yayinda aka fara aikin nemo masu rai a cikin baraguzan gine-gine da suka rubta.

WASHINGTON, D.C. - Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shaida wa taron manema labarai cewa, a kalla mutane 912 ne suka mutu a Turkiyya, yayin da kusan mutane 5,400 suka jikkata. Ya ce ba zai iya hasashen ko adadin zai haura ba yayin da ake ci gaba da aikin ceto, kuma akalla gine-gine 2,800 ne suka ruguje.

Jami’an kiwon lafiya na Syria sun ce akalla mutane 326 suka mutu a yankunan da gwamnati ke rike da su, yayin da masu aikin ceto suka ce akalla wasu 100 sun mutu a yankunan da ‘yan tawaye ke iko da su.

Ministan cikin gida na Turkiyya Suleyman Soylu ya ce an samu aukuwar hucin girgizar kasar har fiye da 20 bayan aukuwar girgizar ta farko kafin wayewar gari.

-VOA/AP

XS
SM
MD
LG