Kanal Sheka yace suna nan suna fafatawa da 'yan Boko Haram kamar yadda aka yi alkawari saboda tabbatar da kawo karshen 'yan ta'adan Boko Haram da kuma ta'adanci gaba daya.
Sojoji na fafatawa dasu a bangarori da dama musamman wuraren da suka jibanci dajin Sambisa da inda aka san sun yi kakagida. Kwanaki sojoji sun kwato Dikwa kuma suna cigaba da sintiri a garin da yankin. Sojojin na kokarin kwato sauran kauyuka da garuruwa dake hannun 'yan ta'adan.
Tun lokacin gwamnatin Jonathan sojojin Najeriya ke ikirarin samun nasara. Yanzu ma a karkashin shugabancin Buhari sojoji na cigaba da buga kirjin samun nasara. To saidai har yanzu fadan ya ki ci yaki cinyewa. Shin wai suna da karfi ne sosai. Kanal Sheka yace sun dade suna aika-aika kuma yawancin mayakansu basu san abun da suke yi ba sai abun da aka sasu su yi, kana kuma gasu da yawa.
Dangane da samar ma sojojin Najeriya kayan aiki da kudade, Kanal Sheka yace ana kokari a basu duk abubuwan da suke bukata. Irin yakin da suke yi da Boko Haram ya kunshi abubuwa da dama da kuma bangarori da yawa. Duk ana kokarin yin aiki tare.
Ban da bukatar kakkabo 'yan Boko Haram ana son a dakile duk hanyoyin da suke samun kudi da makamai da wasu kayan aiki. Wadanda suka tuba ana duba yadda za'a taimakesu. Ana kuma tantance wadanda aka kama tare da yin bincike.
Akan gano daliban Chibok Kanal Sheka yace duk abun da suke ciki zasu sanarda 'yan jarida saboda fadakar da duniya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5