Wannan harin bam ya zo ne kwanaki 3 da tashin tagwayen bama-baman da akalla mutane 20 suka rasu. Talbijin din gwamnati yace wata mace ce ta tada bam din a wani fitattaccen dandalin dare.
Inda hakan ya ankarar da jami’an soji dana ceto suka shiga neman jikatattu. Kamfanin dillancin labarai na Reuters sun ce sun ji wani babban jami’in soja na cewa akalla mutane guda 60 ne suka jikkata.
Ba dai wanda ya dauki alhakkin wadannan hare-hare, amma hukumomin Kamaru na zargin irin hare-haren ‘yan Boko Haram ne na Najeriya.