Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya na dada kutsawa Sambisa


Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya Tukur Yusuf Buratai
Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya Tukur Yusuf Buratai

Rundunar sojojin Najeriya suna dada kutsawa tare da cin ribar yakar ‘yan kungiyar ta’addar Boko Haram a cikin dajin Sambisa.

Kamar yadda kakakin rundunar sojojin Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya sanar. Ya kara da cewa yanzu sunan rundunarsu Zaman Lafiya Dole. Yace sojojin kasar ba zasu karaya da yawan hare-haren da su ‘yan ta’addar ke ta faman kaiwa a wurare daban daban ba.

Ko a shekaran jiya Alhamis sai da suka tada tagwayen bama-bamai suka hallaka akalla mutane 37 a jihar Gombe dake arewacin Najeriya. Kuka Sheka yace, bisa umarnin sabon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, suna kutsawa tare da buda manyan hanyoyin da su ‘yan boko haram suka daddatse.

Sannan yace, sojojin kasar za su ci gaba da bada himmar magance matsalar da ta addabi kowa ta boko haram. Daga karshe ya Kuka Sheka ya gargadi masu ci da yawun sojoji kan cewa zasu dauki mutane aikin soja, da su kuka da kansu. Ya ma tabbatar da damke wasu barayin fasahar shafin sojin kasar na intanet.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG